Ana ci-gaba da zanga-zanga a Venezuela | Labarai | DW | 22.02.2014
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Ana ci-gaba da zanga-zanga a Venezuela

Shugaban Venezuela Nicolas Maduro ya nemi kawo karshen zanga-zangar nuna kiyeyya ga gwamnatinsa sakamakon matsalar tsadar rayuwa da ake fuskanta a kasar.

Shugaban Venezuela Nicolas Maduro ya ce ya na bukatar wata gagarumar tattauawa da Shugaban Amirka Barack Obama sakamoon.zargin jami'an diplomasiyar kasar ta Amirka da kafofin yada labaranta da rura wutar rikicin. Cikin wannan mako gwamnatin kasar ta soke takardun aiki na wasu kafofin yada labaran Amirka tare da sallamar jami'an diplomasiya na kasar uku. Shi dai Maduro ya na fuskantar zanga-zangar nuna kiyeyya ga gwamnati da aka kwashe makonni ana gudanarwa, abun da yake

Mutane takwas sun hallaka yayin da wasu fiye da 130 suka samu raunuka, yayin artabu tsakanin jami'an tsaron kasar ta Venezuela da masu zanga-zanga, wadanda ke neman Shugaba Maduro ya ajiye aiki, saboda yadda ake samun hauhawar farashin kayayyaki da karancin kudaden musanya na kasashen duniya.

Mawallafi: Suleiman Babayo
Edita: Mouhamadou Awal Balarabe