Ana ci gaba da zabe a wasu wurare a Najeriya
March 29, 2015Talla
Kamar yadda hukumar zaben kasar ta sanar, an ci gaba da zabukan ne a yau Lahadi don baiwa saura damar damawa kamar kowa, ta kuma amince da kura-kuran da aka samu na na'urorin tantance masu zabe a jiya.
Najeriya na da rumfunan zabe dubu 150 ne a fadin kasar, kamar mahukunta suka tabbatar.
Zaben na wannan lokaci dai ya ci karo da wasu hare-haren da aka danganta da mayakan kungiyar Boko Haram a arewa maso gabashin kasar, wadanda suka halaka akalla mutane 41, sai kuma wasu mutanen uku ciki har da Soji guda da aka halaka a jihar Rivers da ke a kudancin kasar.