Ana ci gaba da yin zaɓen fida gwani a Amirka | Labarai | DW | 06.03.2016
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Ana ci gaba da yin zaɓen fida gwani a Amirka

A Amirka a zaɓen share fage na takarar shugaban ƙasa Sanata Ted Cruz na jam|iyyar Republican da Bernies Sander na Democrat sun samu nasara a jihohi biyu a zaɓen.

USA Vorwahlen CNN Debatte Trump, Rubio und Ted Cruz

Hotunan Trump, Rubio, da Ted Cruz dukkaninsu 'yan takara a zaɓen fida gwani na Amirka a ƙarƙashin tutar Republican

Sai dai kuma mutanen da ake ganin har yanzu su ne kan gaba wato Donal Trump na jam'iyyar Republican da Hillary clibnton ta Democrats sun ƙara samun ƙwarin gwiwa.

Ted Cruz na Republican wanda ke ci gaba da hasahen ganin zai kai labari a gaban Donal Trump ya samu nasara a jihohi biyu bisa huɗu inda aka yi zaɓen a ƙarshen mako watau Kansas da Maine.Shi kuwa Donal Trump ya samu nasara ne Louisiane da kentucky. A ɓangaran jam'iyyar Republican kuwa Bernie Sander ya doke da Hillary Clinton a jihar Kansas.