Ana ci gaba da yin tashin hankali a Masar | Labarai | DW | 23.07.2013
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Ana ci gaba da yin tashin hankali a Masar

An kashe mutane a ƙalla guda huɗu a artabun da aka sha tsakanin magoya bayan tsohon shugaban ƙasar Muhammad Mursi da kuma masu adawa da shi.

Masu aiko da rahotannin sun ce a unguwar Qaliub da ke a arewacin birnin Alƙahira an kashe mutun biyu. Yayin da wasu majiyoyin tsaro suka ce ɗaya, jirkin ƙasa ya markaɗe shi a lokacin da yake ƙoƙarin tserewa daga dandalin da ake yin bata kashi tsakanin ɓangarorin biyu kana aka harɓe ɗaya har lahira a dandalin Tahrir.

Tun da farko a cikin wata sanarwa da ya sake yi gabannin tashin hankali, shugaban gwamnatin wucin gadi na Masar ɗin Adly Mansur ya yi kira ga haɗin kan al'ummar ƙasar. Hakan kuwa na zuwa a daidai lokacin da iyalen hamɓararren shugaban ke shirin shigar da ƙara a gaban wata kotu taƙasa da ƙassa a kan Janar Abdel Fatah Sisi wanda suke zargi da sace Muhammad Mursi.

Mawallafi : Abourahamane Hassane
Edita : Usman Shehu Usman