Ana ci gaba da tura dakaru domin kawar da ′yan tawayen Mali | Labarai | DW | 18.01.2013
 1. Inhalt
 2. Navigation
 3. Weitere Inhalte
 4. Metanavigation
 5. Suche
 6. Choose from 30 Languages

Labarai

Ana ci gaba da tura dakaru domin kawar da 'yan tawayen Mali

Kungiyar Tarayyar Turai ta amince da tura daruruwan dakaru domin taimakawa wajen haros da dakarun sojan kasar Mali

Kungiyar Tarayyar Turai ta amince da tura daruruwan dakaru domin taimakawa wajen haros da dakarun sojan kasar Mali, karkashin jagorancin Janar Leh-Quantre na kasar Faransa, wanda zai jagoranci aikin na horas da sojojin.

Cikin watan gobe na Febrairu ake fara cikekken aikin, amma cikin kwanaki masu zuwa ake saran tawogar farko ta masu bada taimakon kayan aiki za ta isa Bamako babban birnin kasar ta Mali. Ministan harkokin wajen Jamus Guido Westerwelle ya tabbatar da haka cikin sanarwar da aka fitar.

Ana ci gaba da kai dauki ga kasar ta Mali, inda dakarun Faransa da su ka kaddamar da samame ke ci gaba da sasakan 'yan tawaye, kuma su na samun tallafi daga kasashen Afirka da ke ci gaba da tura sojoji. Sojojin Najeriya, Togo da Chadi na cikin wadanda ke ci gaba da isa, kuma bisa yadda aka tsara dakarun Afirka za su yi aikin karkashin Komandan sojan da Najeriya ta nada. Yayin da Faransa ke kara yawan dakaru da ci gaba da mamaye yankunan kasar ta Mali domin dakile karfin 'yan tawayen da mayar da yankuna karkashin ikon gwamnati.

Mawallafi: Suleiman Babayo

Edita: Halima Balaraba Abbas

 • Kwanan wata 18.01.2013
 • Muhimman kalmomi Mali
 • Bugawa Buga wannan shafi
 • Permalink https://p.dw.com/p/17Mg5
 • Kwanan wata 18.01.2013
 • Muhimman kalmomi Mali
 • Bugawa Buga wannan shafi
 • Permalink https://p.dw.com/p/17Mg5