Ana ci gaba da tashe-tashen hankulla a Bangui | Labarai | DW | 30.05.2014
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Ana ci gaba da tashe-tashen hankulla a Bangui

A kalla mutane biyu ne suka rasa rayukan su daga cikin masu zanga-zanga, a Bangui babban birnin Jamhuriyar Afirka ta tsakiya.

Masu zanga-zangar dai na nuna kyamar su ce ga shugabar rikon kwaryar kasar Catherine Samba Panza, da ma dakarun kiyaye zaman lafiya na kasa da kasa dake ayukan tsaro a wannan kasa.

Daga nasu bengare kungiyoyin mayaka da suka ki su ajiye makammai a wannan kasa, na kai hare-hare ga dakarun kiyaye zaman lafiya na kasa da kasa, a duk lokutan da motocin su ke fucewa cikin birnin Bangui, inda su kuma suka sha alwashin mayar da martani.

Harin baya-bayan nan dai da wasu 'yan bindiga suka kai a wani Coci dake birnin na Bangui, inda aka kashe mutane 17 tare da yin awon gaba da wasu mutanen 27 ne, ya kara tayar da kayar bayan masu zanga-zangar, Inda a wannan Juma'ar ma shugabar kasar ta rikon kwaryar Catherine Samba Panza, tayi Allah wadai da harin da tace na ta'adanci ne.

Mawallafi: Salissou Boukari
Edita : Zainab Mohamed Abubakar