Ana ci-gaba da rusa guraren tarihi a arewacin Mali | Labarai | DW | 24.12.2012
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Ana ci-gaba da rusa guraren tarihi a arewacin Mali

A kasar Mali,kungiyoyin da ke da tsautsauran kishin islama sun dau arwashin ragargaza gine ginen tarihi akan hujar sun sabawa musulunci.

default

Babban matsalacin tarihi a Tumbuktu

A ranar lahadi ne kungiyoyin kishin islaman da ke arewacin Mali, suka aukawa wasu giine ginen tarihin da suka rage a birnin Tombuktu. Kungiyoyin da suka hada da Mujao, da Ansar dine da kuma Aqa'ida a Maghreb masu tsautsauran kishin islama,sun dauki arwashin kaacan kacana duk wasu gine-ginen tarihi da suka hada da makwantan waliyan da ke yankin da kuma gidajen ajiyar littatafan tarihi a kan hujar guraren bauta ne.
Tuni dai kasashen duniya da ma Majalisar Dinkin Duniya suka nuna damuwa, ciki har da komishiniyar harakokin wajen tarayyar Turai Catherine Ashton wacce ta nuna bacin ranta ga abun da ta kira halin dabbobi daga kungiyoyin kishin islaman, inda ta ce addinin musulunci addini ne da ke amfani azahiri da tarihi don haka bai kamata wasu su kafe da shi ba domin cin zarafin al'umma.
Yayin da ministan tsaron Faransa Jean Yves Ledrian ya ce akwai ma yuyuwar aukawa arewacin na Mali kamun wa'adin da Majalisar Dinkin Duniya ta diba, inda ya ce haka na iya faruwa a cikin watannin farko na sabuwar shekara mai shirin kamawa.

Mawallafi: Issoufou Mamane
Edita: Mohammad Nasiru Awal