Ana ci gaba da neman wadanda ke jirgin ruwan Koriya ta Kudu | Labarai | DW | 19.04.2014
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Ana ci gaba da neman wadanda ke jirgin ruwan Koriya ta Kudu

An tsamo gawauwaki 36 na fasinjojin jirgin ruwan Koriya ta Kudu, yayin da ake neman sauran daruruwa da suka nutse a ruwa

Masu aikin ceto na kasar Koriya tav Kudu sun tsamo gawauwakin mutane 36, daga jirgin ruwan kasar da ya kife da fasinjoji mafi yawa 'yan makaranta. Yayin da ake ci gaba da neman fiye da mutane 260 da ke cikin jirgin ruwan.

Mahukuntan kasar ta Koriya ta Kudu sun damke matukin jirgin ruwan, da wasu ma'aikata biyu na jirgin ruwan, saboda sakaci da ficewa daga cikin jirgin ruwan lokacin da ya samu matsala, maimakon su taimaka wa mutanen da hatsarin ya ritsa da su.

Mawallafi: Suleiman Babayo
Edita: Mouhamadou Awal Balarabe