1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Martani kan kisan Fulani a Mali

Abdourahamane Hassane GAT
March 26, 2019

Ana ci gaba da yin kiraye-kiraye na daukar matakin bincike biyo bayan kisan Fulani da 'yan kabilar Dogon maharba suka yi a garin Ogossagou na kasar Mali inda a yanzu adadin mutanen da suka mutu ya kai 160.

https://p.dw.com/p/3FgEj
Zentralafrikanische RepublikTrauer in Bangui
Hoto: Getty Images/AFP/E. Dropsy

Hukumomi a Kasar Mali sun ce addadin mutanen da suka mutu a harin da 'yan kabilar Dogon maharba suka kai a kan Fulani a Ogassagou da ke a yankin tsakiya na kasar cikin lardin Mopti kan iyaka da Burkina Faso ya karu zuwa mutane 160. Yanzu haka dai al'umma a kasar ta Mali na cikin zaman juyayin abin da ya faru. 

Bayanan da ake ci gaba da samu daga kasar ta Mali na cewar 'yan kabilar ta Dogon sun yi kisan kare dangi a kan Fulanin da ke zaune a kauyen Ogossagou da ke cikin jihar Mopti kan iyaka da Burkina Faso lokacin da suka yi dirar mikiya a garin wanda da farko suka barbada man fetir a kan gidajan kwana na mutane da rumbunan ajiye abinci da dabobi kafin daga bisanin su kunna wuta sannan su shiga sasarar jama'ar da takuba da aduna.

Fulani demonstrieren in Bamako, Mali
Hoto: AFP/Getty Images/A. Risemberg

Wannnan al'amari ya kada hankali al'ummar a sauran birnan Mali inda kungiyoyi masu fafutuka da jama'a da 'yan siyasa suka gudanar da taruruka domin yin Allah wadai da harin tare kuma da yin kira ga gwamnatin da ta gaggauta daukar mataki. Moussa Coulbaly wani masanin kimiyar siyasa a Malin ya ce ya zama wajibi a bi hanyoyin tattaunawa domin neman sulhu tsakanin kabilun:

"Ya kamata a girka wata hukuma ta musamun da za ta bude hanyoyin tattaunawa tsakanin kabilun biyu na Dogon da Fulani domin kawo karshen tashin hankalin kwata-kwata ya ce kada a kuskura a nuna ba da fifiko ga kowane bangare wannan shi ne abin jikara"

A Halin da ake ciki babbar alkali mai gabatar da kara ta kotun duniya watau CPI ko ICC Fatou Bensouda  ta yi Allah wadai da harin wanda a ciki aka kashe yara kanana da mata da ma tsofi. Sai dai ba ta ambanto ko akwai wani hukunci da kotu za ta iya yi ba, sai dai kawai ta nuna cewa alhakin hukunci yana a kan kotun Mali. Firaministan Malin da ya kai ziyara a kauyen Ogossagou ya tabbatar wa da al umma cewar za a hukunta wadanda suka aikata ta'asar bayan ya yi musu ta'aziya:

Nigeria Ibrahim Boubacar Keita in Abuja
Hoto: Reuters/A. Sotunde


"Tuni muka dauki mataki a game da batun harin na rusar da kungiyar mayakan da kuma sallamar wasu manyan sojojin kasar ya ce tsaron al'umma ya kamata kowa ya sani cewa yana a kan wuyan gwamnati".

Shima dai minista shariar na Mali Tiena Cooulbaly ya ce za a ba wa gawa kashi domin mai rai ya ji tsoro saboda ya ce za su zakulo wadanda suka aikata kisan ko ina suka shiga domin hukunta su