Ana ci gaba da kai hare-haren kunar bakin wake a Mali | Labarai | DW | 28.09.2013
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Ana ci gaba da kai hare-haren kunar bakin wake a Mali

Sojojin Mali da dama sun sami rauni sakamakon harin kunar bakin wake a yankin arewacin kasar.

Kwamandan wani sansanin soji kasar Mali Kanal Keba Sangare ya bayyana cewa, wasu 'yan harin kunar bakin wake sun mutu yayin da sojoji da dama suka jikkata bayan da maharan suka tashi Bom din da ke jikin motarsu a kusa da sansanin sojin dake arewacin kasar ta Mali.

Wanna dai shi ne karo na biyu da masu harin kunar bakin wake ke kai farmaki kan sansanonin jami'an tsaron kasar, tun bayan da kungiyar 'yan tawayen Abzinawa ta bayyana dakatar da shiga cikin tattaunawar sulhu da gwamnati.

Tun dai a farkon wannan shekarar da muke ciki ne a ka cimma yarjejeniyar fara tattaunawar sulhu tsakanin gwamnatin da 'yan tawayen Abzinawan. Sai dai kuma ranar Alhamis (26. 09. 13) din da ta gabata, 'yan tawayen sun sanar da janyewa daga tattaunawar.

Mawallafiya : Lateefa Mustapha Ja'Afar
Edita : Saleh Umar Saleh