1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Kungiyar SADC ta amince da zaben Kwango

Suleiman Babayo
January 2, 2019

Masu saka ido kan zabe na kungiyar kasashen yankin kudancin Afirka sun nuna gamsuwa da zaben Jamhuriyar Dimukuradiyyar Kwango

https://p.dw.com/p/3AwIs
Kongo hält mit zwei Jahren Verspätung historische Wahlen ab
Hoto: Reuters/R. Carrubba

Masu saka ido kan zabe na kungiyar kasashen yankin kudancin Afirka, SADC, sun bayyana cewa zaben Jamhuriyar Dimukuradiyyar Kwango ya gudana kadaran-kadahan, duk da matsalolin da suka hana mutane da dama kada kuri'a.

Matakin da kungiyar SADC ya yi hannun riga ikirarin 'yan adawa na zargin tafka magudi a zaben na 30 ga watan jiya na Disamba, inda wani dan majalisa na Amirka ya ce babu gaskiya balle adalci. Gaggan 'yan takara a zaben sun hada da Emmanuel Ramazani Shadary na bangaren gwamnati da 'yan adawa da suka hada da Martin Fayulu da Felix Tshisekedi. Shugaba Joseph Kabila na Jamhuriyar Dimukuradiyyar Kwango ya shafe kusan shekaru 18 yana rike da madafun iko kuma zai zama shugaba na farko da ya mika mulki a kasar cikin kwanciyar hankali.

Sai dai yanzu haka an kwace izinin aiki na wani dan jaridan gidan rediyon Faransa na RFI tare da dakatar da watsi shirye-shiryen tashar saboda zaman zullumi da ake ciki sakamakon zaben na Jamhuriyar Dimukuradiyyar Kwango.