An ɗage taron ƙungiyar ƙasashen Larabawa
August 12, 2012Talla
Sanarwa wacce matamaikin magatakardan ƙungiyar, Ahmed Ben Helli ya baiyana, na cewar an dage taron wanda aka so gudanarwa a birnin Djeeddah na Saudiyya,ya zuwa wani lokacin da ba saka rana ba, saboda tiyata da aka yi wa yerima Saoud Al Faycal a ciki, ministan harkokin waje na Saudiyya dake fama da rashin lafiya.
Taron dai, ya so tattauna batun zaɓar mutumin da zai maye gurbin Kofi Annan a matsayin manzan ƙasashen na larabawa da Majalisar Ɗinkin Duniya a Siriya ,wanda wa'adin aikin sa ke kammala a ƙarshen wannan wata.Kuma ana kyautata zaton cewar tsohon ministan harkokin waje na Aljeriya Lakhdar Brahimi shi ne zai gaji Kofi Annan ɗin.
Mawallafi : Abdourahamane Hassane
Edita : Mohammad Nasiru Awal