1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

An zargi sojojin Mali da kisan farar hula

Ramatu Garba Baba
August 10, 2018

Majalisar Dinkin Duniya ta zargi jami'an tsaron kasar Mali da laifin kisan fararen hula, bayan da bincike ya nuna yadda aka yi wa mutanen kisan gilla a yayin wani samamen sojojin kan mayakan jihadi.

https://p.dw.com/p/32wZq
Mali Soldaten
Hoto: Getty Images/AFP/J. Saget

Bincike ya nunar da cewa so uku sojoji suna kai hari ba tare da yin la'akari da rayuwar fararen hula ba. An gano yadda mutum goma sha biyu suka rasa rayukansu a wani hari da sojin suka kai a wata kasuwar shanu dama wasu wurare biyu. Majalisar ta bayyana damuwa kan kisan da ta ce laifi ne da ya keta hakkin bil Adama.

Gwamnatin Mali dia a farko ta daura alhakin kisan kan mayakan jihadi, daga baya ta amince da laifin bayan da aka gano wasu kabura da aka binne gawarwakin mutane, ta kuma ce ta soma na ta binciken kan wannan ta'asa.