An zargi sojojin Kongo(DRC) da cin zarafin mata | Labarai | DW | 12.04.2013
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

An zargi sojojin Kongo(DRC) da cin zarafin mata

A Jamhuriyar Dimukuradiyar Kongo an dakatar da hafsosin soji guda 12 bisa zargen su da ake yi da laifin cin zarafin mutane a yakin da aka gwabza a gabashin kasar.

Rundunar kiyaye zaman lafiya ta Majalisar Dinkin Duniya da ke a Kongo wato MONUSCO ita ce ta ba da sanarwar haka. Ana zargin hafsosin sojin ne da hannu a aika-aikar cin zarafin mutane 126. Akan haka ne ma a taron da suka gudanar a jiya Alhamis a birnin London, ministocin harkokin wajen kasashen G8 suka mika bukatar daukar tsauraran matakai domin yaki da cin zarafin mata a da ake yi a cikin rikice-rikice da kuma wuraren da ake fama da rikici a cikinsu, tare da samar da Euro miliyan 27 domin tabbatar da hakan. Sakataren harkokin wajen Birtaniya, Willian Hague ya ce tun daga shekarar 1996 ne ake samun dubban mata da ke fuskantar cin zarafi ta hanyar yin lalata da su a kasar ta Kongo.

Mawallafiya: Halima Balaraba Abbas
Edita: Usman Shehu Usman