An zargi sojojin Isra′ila da laifukan yaki | Labarai | DW | 28.02.2019
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

An zargi sojojin Isra'ila da laifukan yaki

Sakamakon binciken Majalisar Dinkin Duniya kan zanga-zangar da Falasdinawa suka gudanar a zirin Gaza shekarar data gabata ya zargi sojojin isra'ila da laifukan yaki biyo bayan harbe fararen hular da yawansu ya kai 189.

Wani faifan bidiyo da cibiyar bincike mai zaman kanta karkashin jagorancin hukumar kare hakkin 'dan Adam ta Majalisar Dinkin Duniya ta fitar ya nuna cewa Falasdinawa kimanin dubu shida suka jikkata a lokacin da wasu gwanayen harbi na rundunar sojin Isra'ila suka kaddamar da harbin kan mai uwa da wabi yayin zanga-zangar. Firaministan Israilar Benjamin Netanyahu ya bayyana sakamakon binciken a matsayin yarfe da kuma kin jinin Isra'ila.