An zargi sojin AMISOM da fyade a Somalia
September 8, 2014Talla
A wani rahoto da Human Rights Watch din ta fidda ta ce wasu daga cikin matan da aka yi wa fyaden sun ce sojin sun basu abinci da 'yan kudade domin nuna cewa kamar da amincewarsu suka yi amfani da su.
To sai dai rudunar sojin ta AMISOM ta bakin kwamadanta Janar Silas Ntigurirwa ta musanta wannan zargi da ake wa dakarunta inda ya ce rahoton da Human Rights Watch ta fidda bai yi musu adalci ba kuma ya na cike da gibi matuka.
Mawallafi: Ahmed Salisu
Edita: Mohammad Nasiru Awal