An zantar da hukuncin kisa a Afganistan
November 22, 2012Talla
Hukumomin Afghanistan, sun aiwatar wa wasu mutane shidda hukuncin kisa ta hanyar ratayewa a wannan Larabar. Ministan harkokin shari'ar kasar ne ya bayana sanarwar kashe mutanen jim kadan bayan da aka zartar da hukuncin. An tuhumi mutanen ne da laifin cin amanar kasa bayan da aka same su da hannu a hare haren da suka yi sanadiyar mutuwar a kalla mutane 45, a jerin hare haren da suka kai a birnin Kabul na kasar a shekara ta 2010. Jim kadan kafin zartar da hukuncin, shugabannin Taliban sun yi barazanar daukar fansan mutanensu, indan har aka aiwatar musu da hukuncin na kisa. Kimanin mutane 14 ne aka rataye tun farkon wannan shekarar a kasar ta Afghanistan.
Mawallafi: Issoufou Mamane
Edita: Usman Shehu Usman