An zabi shugaban Mauritaniya a matsayin shugaban kungiyar AU | Labarai | DW | 30.01.2014
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

An zabi shugaban Mauritaniya a matsayin shugaban kungiyar AU

Shugaban kasar Mauritaniya Mohamed Ould Abdel Aziz ya karbi ragamar shugabancin kungiyar tarayyar Afirka na tsawon shekara daya.

A wannan Alhamis din ce, taron karo na 22 dake gudana a birnin Addis Abeba na kasar Habasha ya zabi shugaban kasar ta Mauritaniya a matsayin sabon shugaban kungiyar ta tarayar Afirka na tsawon shekara guda.

Shugaba Abdel Aziz ya canji Hailemariam Desalegn wanda shine Praministan kasar ta Habasha, daga kan wannan mukami na shugaban wannan Babbar kungiya ta Kasashen Afirka.

Da yake magana sabon shugaban kungiyar tarayar Afirka, ya jinjinawa wanda ya canza tare da shan alwashin aiki da membobin wannan kungiya dan ganin cewa Nahiyar Afirka ta samu wurin da ya dace da ita cikin Duniya baki daya.

Taron dai yayi niyar tantamna batun noma da matsalar karancin abinci, amma batun sabon babin rikicin da ake ciki a kasashen Sudan ta Kudu da Jamahuriyar Afirka ta Tsakiya ya mamaye ajandar taron.

Mawallafi:Salissou Boukari
Edita: Umaru Aliyu