An zabi sabon shugaban majalisar bishop na Jamus
March 12, 2014An zabi Kardinal Reinhard Marx na yankin München-Freising a matsayin sabon shugaban taron manyan bishop bishop na darikar Roman-Katolika da ke nan Jamus. Kardinal Marx, da aka zaba a yayin taron bishop-bishop da ke gudana a birnin Münster, zai maye gurbin Archbishop Robert Zollitsch mai shekaru 75 kuma daga birnin Freiburg a dalilan tsufa. Tun daga shekara ta 2008 ne dai ya kasance archbishop, kafin a shekara ta 2010 tsohon Paparoma Benedikt na 16 ya dauke shi a kwalejin kardinal. Mai shekaru 60 da haihuwa, Kardinal Reinhard Marx ya kasance daya daga cikin shugabanni lura da batutuwan da suka danganci rayuwar jama'a na majalisar bishop-bishop a nan Jamus, kuma shi ne shugaban hukumar shugabannin darikar Roman-Katolika na Turai. A watan Afrilun shekara ta 2013 ne dai, Paparoma Francis ya nada shi da wasu kardinal guda 7 a matsayin masu ba shi shawara kan gudanar da darikar. Kazalika a wannan Asabar da ta gabata ne dai, Paparoman ya sanar da nadin Kardinal Reinhard Marx a matsayin mai kula da sabuwar majalisar kula da kudaden majami'ar.
Mawallafiya: Zainab Mohammed Abubakar
Edita : Pinado Abdu-Waba