An zabi sabon shugaban kasar Afrika ta Kudu
February 15, 2018Talla
Wannan ya zo ne a daidai lokacin da rundunar 'yan sandan kasar ta cafke mutane takwa da ke da dangantaka kai tsaye da badakalar cin hanci da karbar rasharawar da tayi awon gaba da mulkin shugaba jacob zuma. Lamarin dai na faruwa ne kwana guda bayan da shugaban kasar Jacob Zuma ya sauka daga karagar mulkin kasar bayan matsin lamba daga jam'iyyarsa ta ANC.