An zabi Li a matsayin Premiyan China
March 15, 2013A wannan Juma'ar ce majalisar dokokin kasar China ta zabi Li Keqiang a matsayin Premiya a hukumance, domin shugabantar wannan kasa ta biyu a bunkasar tattalin arziki. Kamar yadda ake zato wakilan fitacciyar jam'iyyar NPC, sun zabi Li mai shekaru 57 da haihuwa da murya daya, domin maye gurbin Wen Jiabao. Kusan wakilai 3, 000 suka taru a babban dakin taron birnin Beijing, domin zaben Li, wanda ke tabbatar da mataki na karshe na sauya madafan iko. 'Yan majalisar china din uku ne kadai suka kada kuri'ar nuna adawa, a yayin da wasu shida suka ki kada kuri'unsu. A yayin da shugaba Xi Jinping zai kasance jagorar kasar, Li zai shugabanci majalisar wakilai, tare da kula da gudanarwar gwamnati da fannin tattali. Shugabar gwamnatin Jamus Angela Merkel, ta kasance shugabar gwamnatin wata kasar ketare ta farko da ta kira Li, domin taya shi murna. Kazalika sun tattauna matsalolin tattalin arziki dake addabar wasu kasashen Turai.
Mawallafiya: Zainab Mohammed Abubakar
Edita : Usman Shehu Usman