1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

An zaɓi sabon jagoran ɗariƙar Roman Katolika.

March 14, 2013

Jorge Mario Bergoglio, shi ne zai gaji Paparoma BenidiKt na 16, wanda ya yi marabus a cikin watan jiya saboda matsalar tsufa

https://p.dw.com/p/17x61
VATICAN CITY, VATICAN - MARCH 13: Newly elected Pope Francis I appears on the central balcony of St Peter's Basilica on March 13, 2013 in Vatican City, Vatican. Argentinian Cardinal Jorge Mario Bergoglio was elected as the 266th Pontiff and will lead the world's 1.2 billion Catholics. (Photo by Peter Macdiarmid/Getty Images)
Hoto: Getty Images

Manyan limaman Cocin ɗarikar Roman Katolika sun zaɓi Kardinal Jorge Mario Bergoglio, bayan kwashe kwanaki biyu ana kaɗa ƙuri'a, Mario wanda ya ɗauki sunnan Paparoma Francis, na da shekaru 76 a duniya. Kuma an haife shi a birnin Buenos Aires na Argentina, kana shi ne wani mutumin na farko na yankin Latine Amurika da aka zaɓa ɗan ɗarikar Jesuite.

Jum kaɗan bayan fitar farin hayaƙi an baiyana sunnansa, Paparoma ya yi jawabi ga dubun dubatar jama'ar da suka yi dandazo a dandanli Saint Peter.Ya ce ''Ina kira gareku da ku yi mani dua'i Allah ya yi mana jagora a kan wannan nauyi.'' Yau aka shirya zai gudanar da fitarsa ta farko a Cocin na Katolika sannan ya ziyarci tsohon Paparoman. Masu lura da al'ammura na hasashen cewar ya na da manyan ƙalubale a gabansa dangane da badaƙalar lallata da yara da wasu limaman Cocin suka riƙa yi.

Mawallafi : Abdourahamane Hassane
Edita : Saleh Umar Saleh.