An yi zanga-zanga ƙin manufofin shugaba Hugo Chavez
May 20, 2007Talla
Dubun dubatan mutane sun gudanar da zanga-zanga a Caracas babban birnin kasar Venezula don nuna adawa da shirin shugaba Hugo Chavez na rufe wata tashar telebijin mai zaman kanta. Tashar da ake kira RCTV ta kulla kawance da ´yan adawa. Shugaba Chavez na zargin tashar da nuna goyon baya da wani yunkurin yi masa juyin mulki da bai yi nasara ba a shekara ta 2002. Shugaban na shirin maye gurbin tashar da wata tashar telebijin ta gwamnati. Masu zanga-zanga na ganin wannan shiri a matsayin babban koma baya ga demukiradiyya.