1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

An yi tir da halin 'yan siyasa a Tunisiya

Mouhamadou Awal Balarabe
January 26, 2021

Matasa sun yi ta jifan ‘yan sanda da duwatsu a lokacin da suka killace majalisar dokokin Tunisiya don hana su shiga. Masu zanga-zanga na neman 'yan siyasa da jami'an tsaro sun gyara halinsu.

https://p.dw.com/p/3oSAJ
Tunesien | Proteste in Sidi Bouzid | Arabischer Frühling
Hoto: Riadh Dridi/AP Photo/picture alliance

Daruruwan 'yan Tunisiya sun gudanar da zanga-zanga a kusa da zauren majalisar dokokin kasar, don nuna rashin jin dadinsu kan halayyar 'yan siyasa da karfi da 'yan sanda ke amfani da shi a kan fararen hula. Wannan na zuwa ne a daidai lokacin da ake muhawara a majalisar kan wani garambawul da gwamnati ke yi don kwantar da  kurar rikicin siyasa da ake fama da shi a kasar. Sai dai masu zanga-zangar ba su samu damar isa harabar majalisar ba saboda tsauraran matakan tsaro da aka dauka.
 
Tuni ma wasu 'yan majalisar suka nuna adawa da wannan matakai, inda suka ce a hanzarta tattaunawa da masu zanga-zanga domin ka da ya lalace zamantakewa tsakanin talakawa da 'yan siyasa. Masu zanga-zangar sun yin tir da dabarun danniya da 'ysan sanda suka yi amfani da shi a lokacin boren juyin juya hali na Janairu 2011 shekaru 10 ke nan da suka gabata.

Matasa sun yi ta jifan ‘yan sanda da duwatsu a lokacin da suke sintiri don aiwatar da dokar hana fita da aka sanya saboda dalilai na kiwon lafiya. ‘Yan sanda sun yi amfani da hayaki mai sa hawaye don tarwatsa su.