1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Ruwan harsashi kan masu zanga-zanga

Yusuf Bala Nayaya
June 14, 2019

Rikicin dai ya balle a Jamhuriyar Bene a wannan Juma'a bayan kwanaki hudu na zanga-zanga kan batun zaben 'yan majalisa na watan Afrilu.

https://p.dw.com/p/3KUdb
Benin Cotonou | Protest der Opposition gegen Ausschluss von Wahl
Hoto: Getty Images/AFP/Y. Folly

Sojoji sun bude wuta a lokacin wata taho mu gama da masu zanga-zanga a Jamhuriyar Bene da ke yankin Afirka ta Yamma. Rikicin dai ya balle a wannan Juma'a bayan kwanaki hudu na zanga-zanga kan batun zaben 'yan majalisa na watan Afrilu kamar yadda wadanda suka sheda lamarin suka nunar.
An dai jibge jami'an tsaro a kusan ko'ina a manyan tituna inda suke kawar da shingaye da aka kafa a garuruwan Save da Tchaourou da ke tsakiyar kasar. Sojojin sun rika amfani da bindiga da harsashin gaske sa'ilin da rikicin ya kai kololuwa.