An yi musayar wuta tsakanin ′yan tawaye da sojoji a arewacin Mali | Labarai | DW | 21.05.2014
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

An yi musayar wuta tsakanin 'yan tawaye da sojoji a arewacin Mali

Wannan tashi hankali dai ya zo ne kwanaki hudu bayan wani artabu tsakanin 'yan awaren Abzinawa da sojojin gwamnati a Kidal inda aka yi asarar rayuka.

A wannan Larabar sojojin Mali sun yi musayar wuta da sojojin sa kai na 'yan tawayen Abzinawa a Kidal da ke zama cibiyar 'yan tawayen arewacin kasar ta Mali, lamarin da ya dagula 'yan kwanciyar hankalin da aka samu biyo bayan mummunar arangamar da aka yi a karshen mako da ya yi sanadiyyar rayukan mutane da yawa. Wani mazaunin yankin ya fada wa kamfanin dillancin labarun AFP ta wayar tarfo cewa mutane na yi ta harbi. Sojojin Mali suna harbi sannan su kuma 'yan tawayen Abzinawa suna harbi. Wani mazaunin garin kuma ya ce harbin ya fi fitowa daga sojoin kasar. Wata majiyar dakarun Majalisar Dinkin Duniya a Mali wato MUNISMA ta tabbatar da barkewar musayar wutar, wadda ta zo kwanaki hudu bayan wani artabu da bangarorin biyu suka yi lokacin ziyarar Firaminista Moussa Mara a Kidal.

Mawallafi: Mohammad Nasiru Awal
Edita: Usman Shehu Usman