An yi kira ga marikitan kasar Somalia da su tsagaita wuta | Labarai | DW | 26.12.2006
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

An yi kira ga marikitan kasar Somalia da su tsagaita wuta

Kungiyar tarayyar Afirka AU ta yi kira da a kawo karshen tashe tashen hankula a Somalia nan take. Shugaban AU Alphar Omar Konare yayi kira ga sojojin sa kai na ´yan Islama da gwamnatin wucin gadi da su tsagaita wuta kana kuma su koma kan teburin sulhu. Rikicin Somalia dai ya kara tabarbarewa bayan da Ethiopia ta kaddamar da yaki akan mayakan Islama na Somalia, inda a jiya ta ruwan bama-bamai akan filin jirgin saman birnin Mogadishu dake hannun ´yan Islaman. KTT ta yi tir da wannan rikici kana ta yi gargadi game da yaduwar fadan a yankin kahon Afirka gaba ki daya. Kwamishinan raya kasashe masu tasowa na kungiyar EU Louis Michel ya nuna damuwa da tsoma bakin da Ethiopia a cikin rikicin na Somalia.