An yi harbe-harbe a Hukumar SSS a Najeriya | Labarai | DW | 30.03.2014
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

An yi harbe-harbe a Hukumar SSS a Najeriya

Hukumar tsaro ta farin kaya wato SSS ta bayyana cewar ta shawo kan harbe-harben da manyan bindigogi da aka fuskanta a cibiyarta da ke a Abuja.

Jami'ar yaɗa labarai ta hukumar tsaron ta SSS Merlyn Ogar ta sanar da cewar harbe- harben sun faru ne bayan da wani fursuna ya yi ƙoƙarin karɓe bindigar da ke hannun mai ba shi abinci a ƙoƙarin da ya yi na arcewa daga inda ake tsare das shi.

To sai dai bayanai sun nuna cewar irin ƙarar bindigar da aka riƙa ji na jefa shakku a kan ko yunƙuri ne na arcewar fursunoni a wurin. Malam Aminu Muhammad wani mazauni kusa da unguwar ya bayyana cewar sun kaɗu matuƙa a sakamakon harbe-harben manyan bindigogin.

Mawallafi : Suleiman Babayo
Edita : Abdourahamane Hassane