An yi garkuwa da mutane a Philippin
June 21, 2017Talla
Rahotanni daga kasar Philippin na cewa wasu mayakan kungiyar Biff ta masu da'awar jihadi sun kutsa a cikin wata makarantar firamare ta birnin Pigkanawayan a wannan Laraba inda suka yi garkuwa da tarin farararen hula.
Tun da sanyin safiyar ne dai mayakan 'yan jihadi kimanin 100 suka kai farmaki kan wata cibiyar sojojin kasar kafin daga bisani wasu kimanin 30 daga cikinsu su kutsa a cikin makarantar inda suka yi garkuwa da mutanen da ke ciki tare kuma da jan daga.
Birnin na Pigkawayan na a nisan kilomita 160 da birnin Marawawi na tsibirin Mindanao wanda mafiyawancin al'ummarsa Kiristoci ne.
Sama da wata dayakenan yankin yake fuskantar jerin hare-haren masu kaifin kishin Islama da ke da'awar yin mubayi'a ga Kungiyar IS.