1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

An yi garambawul a kasar Ghana

Rahmatu Abubakar Mahmud MA
August 10, 2018

A kasar Ghana shugaban kasar Nana Akufo Ado, ya yi garambawul ga wasu daga cikin ministocinsa a karon farko tun hawansa kan karagar mulki. 

https://p.dw.com/p/32yOc
Ghana oppositioneller Kandidat Nana Akufo-Addo
Hoto: picture-alliance/AP Photo/S. Alamba

Wannnan garambawul ya shafi ministoci 15, amma uku daga cikinsu ministoci su ne suka fi daukar hankulan jama'a domin kuwa sun taka muhimmiyyar rawa a ma'aikatarsu na dai. Alal misali ministan ma'aikatar harkokin jirage a karkashinta ne dai aka fadada filin jirgin kasar kana ta farfado da kwangilar jirgin kasar Namibia.

Shi kuwa ministan filaye da albarkatun karkashin kasa ya yi kokarin hana hako ma'adinai ba bisa ka'ida ba tare da kawo tsari wajen mallakar filaye da a baya kan dauki shekaru aru-aru amma yanzu cikin dan karamin lokaci za ka iya samun takardun filinka, sai kuma sashen makamashi.

Textilien aus Ghana - Original und Fälschung
Hoto: DW/Isaac Kaledzi

Wannan sauyi ka iya shafar harkokin kasuwanci wanda kuma zai iya kawo tsaiko ga tattalin arzikin kasar ta Ghna kamar yadda jama'a ke gani. Su ma 'yan jamm'iyyar adawa na ganin babu wani abin azo a gani da wannan garambawul din zai yi.

Yanzu dai abin jira shine ganin cewar majalisar dokoki ta zanta da sabin ministoci da aka zaba don tabbatar da cewar ko zasu iya cimma buri.