An yi babban hadarin jirgin ruwa a kasar Sin. | Labarai | DW | 02.06.2015
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

An yi babban hadarin jirgin ruwa a kasar Sin.

Masu aikin ceto na ci gaba da neman mutanen da suka nitse sakamakon hadarin jirgin ruwan kasar Sin mai dauke da mutane sama da 450 a yankin Hubei a tsakiyar kasar.

Wani jirgin ruwa dauke da mutane a kalla 458 ya nitse a yammacin jiya Litinin (01.05.2015) a kogin Yangzi da ke a matsayin kogi mafi tsawo a kasar Sin, inda kawo yanzu a kalla mutane 13 ne kacal aka samu ceto wa, cikinsu har da jagoran matukan jirgin da kuma wani bakaniken jirgin. Mutanen da ke cikin jirgin ruwan dai 'yan kasar ta Chine ne, kuma akasarinsu tsofaffi ne 'yan shekaru 50 zuwa 80 da haihuwa masu yawon buda ido. Daga cikin wannan adadi dai na mutanen da ke cikin jirgin, ma'aikatan jirgin su 47 ne yayin da sauran mutanen 406 tsofaffin ne 'yan yawon buda ido. Firaministan kasar ta Sin Li Keqiang zai kai ziyara a wurin da hadarin ya auku da ke cikin jihar Hubei a tsakiyar kasar. A cewar hukumomin ruwan kasar ta Sin, jirgin ruwan ya yi gaggawar nitsewa ne bayan da gamu da hadarin ta dalilin rishin kyawon yanayi.