An yanke hukunci ga mutane hudu da suka yi yunkuri kashe mai adawa da shugaba Kagame | Labarai | DW | 10.09.2014
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

An yanke hukunci ga mutane hudu da suka yi yunkuri kashe mai adawa da shugaba Kagame

Ana dai zargin gwamnatin Shugaba Paul Kagame na Ruwanda da farautar masu adawa da ita tana yi musu kisan dauki dai-dai a ketare.

Wata kotu a Afirka ta Kudu ta yanke wa wasu mutane hudu da ake zargi da kokarin kashe mai sukar lamirin shugaban Ruwanda Paul Kagame, hukuncin daurin shekaru takwas kowanensu. Sai dai alkalin kotun Magistrate Mkhari ya ce ba su ne ainihin masu laifi ba.

"Ba ku ne manyan wadanda suka aikata laifi a wannan lamari ba. A gani na kamata ya yi ku gurfana gaba na da dukkan mutanen da suka samar da kudi suka biya ku domin ku aikata wadannan laifuffuka."

Tsohon babban hafsan sojojin Ruwanda Faustin Kayumba Nyamwasa ya samu rauni bayan an harbe shi a ciki lokacin da yake hanyar zuwa gidansa a birnin Johannesburg a shekarar 2010, bayan ya tsere daga Ruwanda saboda rashin jituwa tsakaninshi da Shugaba Kagame. Ana dai zargin gwamnatin Ruwanda da hannu a kokarin kashe masu adawa da ita a ketare, sai dai ta musanta wannan zargi.