1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

An yaba wa WHO a kan cutar Ebola a Kwango

Zulaiha Abubakar
May 25, 2018

Wannan yabo ya biyo bayan matakin gaggawar da ta dauka kan sake bullar cutar Ebola a Jamhuriyar Demokaradiyyar Kwango kamar yadda Peter Salama shugaban sashen gaggawa na hukumar ya sanar.

https://p.dw.com/p/2yLWV
DR Kongo Ebola Ausbruch
Hoto: Reuters/K. Katombe

Sanarwar ta kuma kara da cewar hukumar ta tanadi dukkan kayan da za a bukata wadanda suka hada da kudi don shirin ko ta kwana a yankin Bikoro wanda a halin yanzu yake da mutane hamsin da biyu wadanda binciken likitoci ya tabbatar da sun kamu da cutar ta Ebola tare da mutuwar mutane ashirin da biyu.

A wani ci gaban kuma gwamnatin kasar na ci gaba aikin rigakafin cutar cikin wani shirin hadin gwiwa tsakaninta da jami'an Hukumar Lafiya ta Duniya da kuma wasu kungiyoyi masu zaman kansu.