An wayi gari da harbe-harbe a Kinsasha | Labarai | DW | 20.12.2016
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

An wayi gari da harbe-harbe a Kinsasha

Ofishin kare hakkin bil Adama na MDD a Kwango ya ce mutane 28 aka kama a Kinsasha, 46 a biranen Gabashi na Goma da Bukavu sakamakon adawa da tazarcen Shugaba Joseph Kabila.

An ji karar harbe-harbe a birnin Kinsasha na kasar Kwango da sanyin safiyar Talatan nan, abin da ke zuwa bayan da Shugaba Joseph Kabila ya nuna alamun kin taba kasa daga mulkin wannan kasa, bayan cikar wa'adin mulkinsa a ranar Litinin. An dai rika jin karar bindigogi a wannan birni mai yawan jama'a da suka kai miliyan goma bayan da a manyan yankunan Arewacin kasar biyu aka fara jin karar busa usir alamun da ke nuna kiran 'yan adawa a fito zanga-zanga.

Karar busa usir dai da buga ganguna alamu ne na daga jan kati ga Shugaba Kabila dan shekaru 45 da ya jagoranci kasar tun daga shekarar 2001 ya bar wannan mulki. Sai a daren na ranar kafar talabijin ta kasar ta bada bayanan shugaban na kafa sabuwar gwamnati bisa jagorancin Sami Badibanga da ya yi tawaye daga babban kawancen adawa da gwamnatin Kabila bisa jagorancin Etienne Tshisekedi dan shekaru 84.

An dai ji karar ababan fashewa a yankin Gombe yankin da fadar shugaban kasa ta ke, an kuma ta harba hayaki mai sa hawaye, sai dai babu tabbaci kan wa ke da alhaki na yin harbe-harben. An dai shiga rudani a wannan kasa bayan da tattaunawa tsakanin gwamnati da 'yan adawa ta shiga hali na rashin tabbas, abin da ake fargabar zai iya sanadi na tada hankula a wannan kasa mai albarkatun karkashin kasa.