An wanke Oscar Pistorius da aikata kisa da ganganci | Labarai | DW | 11.09.2014
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

An wanke Oscar Pistorius da aikata kisa da ganganci

Shi dai Oscar Pistorius tun da fari ya ce bai kashe budurwar ta shi mai karatun digiri a fannin shari'a Reeva Steenkamp cikin sani ba.

Alkali da ke sauraren shari'ar da ake yi wa fitaccen dan wasan tseren nakasassun nan Oscar Pistorius wato Thokozile Masipa, ta ce ba bisa ganganci ba ne ya harbe budurwarsa Reeva Steenkamp. Ta ce masu gabatar da kara sun gaza gabatar da cikakkun shedun cewa, fitaccen dan tseren ya kudiri aniyar kashe budurwar tasa da gangan a ranar masoya ta Valentines a shekarar bara.

Mr Pistorius dai ya amince da harbe budurwarsa Reeva Steenkamp a gidansa da ke birnin Pretoria a Afrika ta Kudu a shekarar da ta gabata, sai dai ya musanta aikata harbin da gangan inda ya ce ya dauka wani ne ya masa kutse dalilin da ya sa ya yi harbin kenan.

Sai dai duk da wannan hukunci na wanke shi daga laifuka har guda biyu cikin caje-cajen da ake masa, laifin kisan cikin rashin sani da sakaci na iya kai shi ga daurin shekaru 15.

Za dai a ci gaba da sauraron hukunci da zai nuna makomarsa a ranar Jumma'a.