An tsige Firaminista Somaliya | Labarai | DW | 06.12.2014
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

An tsige Firaminista Somaliya

'Yan majalisar dokoki a Somaliya sun kada kuri'ar tsige Firaministan kasar Abdiweli Sheikh Ahmed daga kan mukaminsa.

Wannan matakin dai ya biyo bayan sabani da aka samu dangane da yiwa majalisar zartaswar kasar kwaskwarima tsakaninsa da Shugaba Hassan Sheikh Mohamud. Kakakin majalisar dokokin kasar ta Somaliya Mohamed Sheikh Osman Jawari ne ya sanar da hakan inda ya ce 'yan majalisa 153 ne suka kada kuri'ar tsige Firaministan da gwamnatinsa baki daya, yayin da wasu 80 kuma suka kada kuri'ar mara masa baya. Wannan dai shine karo na biyu a kasar ta Somaliya da ake tsige Firaminista daga kan mukaminsa a tsahon kasa da shekara guda, a kasar da ke fama da hare-haren ta'addanci daga kungiyar 'yan ta'addan al-Shabab da ke da alaka da al-Qa'ida.

Mawallafiya: Lateefa Mustapha Ja'afar
Edita: Usman Shehu Usman