An tsawaita zabe a wasu sassan Jamhuriyar Nijar | Siyasa | DW | 22.02.2016
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Siyasa

An tsawaita zabe a wasu sassan Jamhuriyar Nijar

A Jihar Damagaram kamar Tahoua da Tillabery a wannan Litinin aka gudanar da zabubukan shugaban kasa da 'yan majalisar dokoki a wasu wurare sakamakon rashin fara zaben ranar Lahadi a kan lokaci.

Ana ci gaba dakon sakamakaon zaben kasar Jamhuriyar Nijar wanda aka tsawaita a wasu sassa na kasar. Tuni kungiyar Tarayyar Afirka ta nuna gamsuwa da yadda zaben ke gudana a kasar da ke yankin yammacin Afirka.

Tuni 'yan adawa suka yi gargadi kan bisa cewa Shugaba Mouhamadou Issougou da ke neman wa'adi na biyu na mulki ya guje wa duk wani yunkuri na magudi domin samun nasara a zagayen farko na zaben.

Bisa tsarin kasar dan takara zai samu nasara a zagayen farko idan ya samu fiye da kashi 50 cikin 100 na kuri'un da aka kada, idan babu wanda ya samu wannan adadi sai a tafi zagaye na biyu na zabe.

Sauti da bidiyo akan labarin