An tsaurara matakan tsaro a Birtaniya | Labarai | DW | 24.05.2017
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

An tsaurara matakan tsaro a Birtaniya

Gwamnatin Birtaniya ta karfafa matakan tsaro a duk fadin kasar bayan da aka kai ga tantance mutuman da ya kai harin kunar bakin wake a wani gidan rawa na birnin Manchester

 

Gwamnatin Birtaniya ta karfafa matakan tsaro a duk fadin kasar bayan da aka kai ga tantance  wanda ya kai harin kunar bakin wake a wani gidan rawa na birnin Manchester a ranar Litinin da ta gabata da ya yi sanadiyyar mutuwar mutane 22.

Firaministar Birtaniya Theresa May ta ce sun dauki matakin ne bayan da sakamakon bincike ya gano cewa akwai yiwuwar kasar ta sake fuskantar wani hari ta'addancin a kowane lokaci daga yanzu. 

Sabbin matakan tsaron dai sun tanadi baza jami'an tsaro da suka hada da sojoji a tashoshin motoci da na jiragen kasa da kuma a filayen jiragen sama da filayen wasanni da wuraren shakatawa.

Kwamishinan 'yan sandar birnin na Manchester Lan Hopkin ya shaida wa manema labarai cewa mutumin da ya kai hari wani matashi ne mai shekaru 22 dan asalin kasar Libiya da ke da takardar dan kasa a Birtaniyar mai suna Salman Abedi.