An tsare Shugaban kasar Gwatalama da ya ajiye aiki | NRS-Import | DW | 04.09.2015
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

NRS-Import

An tsare Shugaban kasar Gwatalama da ya ajiye aiki

Alejandro Maldonado ya zama sabon shugaban kasar Gwatamala bayan Otto Perez ya yi murabus bisa tuhumar cin hanci, yayin da ake shirin zaben kasa baki daya ranar Lahadi mai zuwa.

Kotun kasar Gwatamala ta bayar da umurnin tsare tsohon Shugaban kasar Otto Perez wanda ya ajiye aiki, kuma ake tuhuma bisa zargin cin hanci da rashawa. A wannan Alhamis da ta gabata Perez ya ajiye aiki, kwana daya bayan majalisar dokoki da tube masa rigar kariya. Perez dan shekaru 64 da haihuwa, ya musanta zargin da ake masa, yayin da masu zanga-zanga domin nuna adawa da cin hanci suka nuna farin cikin halin da ake ciki.

Tuni aka rantsar da Mataimakin shugaban kasar Alejandro Maldonado domin karasa wa'adin zuwa watan Janairu mai zuwa, kuma jibi Lahadi ake gudanar da zaben shugaban kasa, dama tsohon Shugaba Otto Perez da ya ajiye aiki, baya da izinin sake takara karkashin tsarin mulkin kasar ta Gwatamala.