An tsagaita buɗe wuta a Ukraine | Labarai | DW | 06.09.2014
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

An tsagaita buɗe wuta a Ukraine

'Yan aware na gabashin Ukraine masu goyon bayan Rasha na mutunta yarjejeniyar tsagaita buɗe wutar da aka cimma a Minsk babban birnin ƙasar Belarussia .

Yarjejeniyar wacce ta fara aiki tun jiya Jagoran 'yan tawayen Alexandre Zakhartchenko, ya ce wata dama ce ga ƙasar ta Ukraine.

''Dakatar da buɗe wutan zai sa a tsirar da rayukan jama'a, sai dai kuma har yanzu muna nan a kan bakamun na warewa daga Ukraine.''

Kuma duk da yarjejeniyar da aka cimma, ƙasashen Ƙungiyar EU sun amince su ƙara ƙaƙabawa Rasha wani ƙarin takunkumin karya tattalin arziki.

Mawallafi : Abdourahamane Hassane
Edita : Usman Shehu Usaman