An tasamma binciken kasafin kudin Nijar | Siyasa | DW | 09.02.2018
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Siyasa

An tasamma binciken kasafin kudin Nijar

A Jamhuriyar Nijar kungiyoyin farar hula da wasu kungiyoyin Afirka sun gudanar da wani nazari tare da bincike kan yanda hukumomin kasashen Afirka ke gaza saka haske a cikin kasafin kudin da suke yi wa kasashensu.

Niger Niamey Opposition (DW/M. Kanta)

Masu fafutuka a Jamhuriyar Nijar

Kungiyoyin sun ce galibin kasashen da suka gudanar da nazari a kansu, gwamnatocin suna nuku-nuku da kasafin kudin musamman ma a fannonin kyautata jin dadin rayuwar jama’a domin kada ‘yan kasa su bi sau da kafa kan ababen da aka tanada wa jama’a, lamarin da ke haifar da koma baya ga Demokradiyya. Rahoton mai kunshe da shafuka da dama da kuma aka gudanar da nazarinsa a cikin kasashe fiye da 100, ya bayyana karara irin yanda sauran kasashen duniya ke tafiyar da kasafin kudadensu ta hanyar amfani da fasahohin bayyana wa al’umomin da suke jagoranta matakan da suka shirya dominsu a cikin kasafin kudin.

Niger Demonsration für Bildungsreform (picture-alliance/AA/B. Boureima )

Taron talakawa masu zabe a Nijar

Sai dai duk da iya ci gaban da aka bayyana samu a wasu kasashen na yammacin Afirka kamar su Burkina Faso da Cote d’ivoire da Senegal da Mali da Chadi da kuma Jamhuriyar Nijar, na daga cikin kasashen da suke Utal wajen bayyana haske a cikin kasafin kudi na kasa da suke wallafawa shekara zuwa shekara. A Jamhuriyar ta Nijar dai kungiyoyin farar hular sun jima da wallafa rahoton dake kokawa da wannan matsayi na nuna halin ko oho da gwamnatin ke yi wa talakawa ta fannin kasafi na kudi. Malam Boubakar Iliassou jigo ne a cibiyar da ke nazarin kasafin kuidi na kasa da saka haske akai wato Rotab

Ya ce ''wani lokacin suna wallafawa wasu lokutan kuma ba duka suke wallafawa ba, kuma cewa aka yi ai idan har ta wallafa to ta wallafa su ta yanda kowane dan kasa zai iya ganinsu ya samu bayanai, abin da bata taba yi ba kenan. Yau idan kana son ka samu wata karda da ta kunshi kasafin kudi ko wani rahoto daga gwamanti, sai ka galabaita baka samu komai, abin zai zame maka tashin hankali ka yi ta zuwa kana dawowa'' 

Ko baya ga rashin saka haske ga kasafin kudi a Nijar kungiyoyin da suka wallafa rahoton sun kuma koka da yanda suka lura da ja bayan gwamnati wajen tanadin kudi da suka kamata a fannonin da ‘yan kasa ke dogaro da su. Malam Moussa Tchangari jagoran kungiyoyin Alternative ne.

Moussa Tchangari, Journalist und Menschenrechtler (DW/ Thomas Mösch)

Moussa Tchangari, jagoran Alternative

Ya ce ''kashi 25 cikin dari ya kamata a saka a cikin harkokin ilimi da horo daga cikin kasafin kudin, kamar yanda Issoufou ya yi alkawali, to har a yanzu kashi 12 ne kawai bai ma kai rabin abin da aka yi alkawali ba da ake sakawa a fannin kiwon lafiya har yau bai kashi 6 cikin dari, hakan idan ka dauki noma da kiwo idan ka dauke shi bai wuce kashi 6 cikin dari ba, alhali kuwa kashi 80 cikin dari na al’umar kasar ke dogaro da harkokin''