An tarwatsa masu zanga-zanga a Washington | Labarai | DW | 01.06.2020
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

An tarwatsa masu zanga-zanga a Washington

Masu zanga-zangar adawa da wariyar launin fata da jami'an tsaro ke nuna wa bakar fatar Amirka sun ci karo da fushin 'yan sanda a gaban fadar mulki ta White House da ke Washington.

‘Yan sandan Amirka sun yi amfani da hayaki mai sa hawaye a gaban Fadar mulki ta White House da ke birnin Washington, don tarwatsa zanga-zangar adawa da wariyar launin fata da jami'an tsaro ke nuna wa bakaken fata a kasar. Su dai masu zanga-zangar sun ta rera kalamai batanci tare da rike allunan da kuma kunna wuta bayan da suka hallara a gaban gidan Shugaban Amirka Donald Trump domin nuna bacin ransu da mutuwar George Floyd bayan cin zarafi da ya fuskanta daga 'yan sanda farar fata.

An kafa dokar-ta-baci a birnin Washington da wasu manyan biranen Amirka, don hana fashe-fashe a zanga-zangar da duban mutane suka halarta a fadin kasar. Duk da cewa wasu shugabanni na cewa sun fahimci fushin masu zanga-zanga, da yawa daga cikin su sun bukaci masu zanga-zangar da su daina lalata dokiyoyi a daidai lokacin da aka shiga kwana ta shida a jere na nuna bacin rai.