An tarwatsa magoya bayan Morsi a Masar | Labarai | DW | 13.08.2013
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

An tarwatsa magoya bayan Morsi a Masar

Magoya bayan tsohon shugaban Masar Mohamed Morsi da masu adawa da shi sun yi fito na fito tsakaninsu. Lamarin da yasa 'yan sanda amfani da karfi wajen shiga tsakani.

'Yayan Kungiyar 'Yan Uwa Musulmi sun yi arangama da magoya bayan gwamnatin Masar da ke ciki a yanzu, inda suka yi ta jifar junansu da duwatsu a tsakiyar birnin Alkahira. Babu dai alkaluma game da adadin da suka jikata, amma kuma rahotannin sun nunar da cewar mata da kananan yara sun tsere domin tsira da rayukansu. 'Yan sanda sun yi amfani da barkono mai sa hawaye wajen shiga tsakanin bangarorin biyu da ke gaba da juna.

Su dai magoya bayan Hambararen shugaban Masar suna ci-gaba ne da gangami domin tilasta wa hukuhamin kasar sakin Mohamed Morsi tare da mayar da shi kan karagar mulki. Makwani shida ne dai aka shafe a Masar ana kai ruwa rana tsakanin 'Yan Uwa Musulmi da kuma bangaren gwamnatin rikon kwarya. Sojojin wannan kasa suna ci-gaba da barazanar amfani da karfin tuwo wajen tarwatsa zaman dirshen da magoya bayan Mohamed Morsi ke yi. Sai dai jami'an dipolomasiya na jan hankalin mahukunta kan bukatar kaucewa tashin hankali da kuma zubar da jini.

Mawallafi: Mouhamadou Awal
Edita: Saleh Umar Saleh