1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

An tarwatsa masu zanga-zanga a birnin Kinshasa

January 20, 2015

Rahotanni daga Kinshasa babban birnin Jamhuriyar Demokradiyyar Kwango na cewa, jami'an tsaro sun yi harbi ta sama a kokarin da suke na tarwatsa masu zanga-zanga da suka fito a rana ta biyu.

https://p.dw.com/p/1ENHq
Hoto: Kannah/AFP/Getty Images

Masu zanga-zangar dai, na nuna kin amincewar su ce ga kwaskwarima kan kundin zaben kasar, wanda kan iya haddasa dage lokacin zaben shugaban kasar da ta kamata ya gudana a shekara mai zuwa 2016. Dalibai da suka fito domin zanga-zangar, sun kona tayoyi da kuma dasa shinge bisa hanyar da ke zuwa jami'ar ta Kinshasa da ke kudancin birnin. A kashen makon da ya gabata ne dai majalisar dokokin kasar ta amince da tsarin yi wa kundin zaben kasar kwaskwarima, wanda a yanzu haka ake tattaunawa a kansa a majalisar dattawan kasar.

A ranar Litinin ma dai (19.01.2015) a kalla mutane hudu ne suka rasu cikinsu har da dan sanda guda, sakamakon artabun da aka yi tsakani jami'an tsaro da masu zanga-zangar, wadanda ke ganin cewa wani salo ne na gwamnati na gyarawa shugaban kasar Joseph Kabila hanyoyin tsayawa kan mulkin kasar.

Mawallafi: Salissou Boukari
Edita : Usman Shehu Usman