An taƙaita zirga-zirga a wasu ƙananan hukumomin Adamawa | Labarai | DW | 02.03.2014
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

An taƙaita zirga-zirga a wasu ƙananan hukumomin Adamawa

Dokar ta zama wajibi ne dan inganta tsaro a ƙananan hukumomin Michika da Madagali inda aka kai hari. A maƙociyar Adamawan kuma wato Borno, an kai sabon hari a ƙauyen Mainok

Murtala Nyako

Gwamnan Adamawa, Murtala Nyako

Rundunar Soji ta 23 dake Yola ta sanar dokar takaita zirga-zirga a kananan hukumomin Michika da Madagali dake arewacin jihar Adamawa.

Wannan sanarwar da Capt. Ja'afaru Nuhu ya fitar a wannan lahadi, na cewa jama'a za su dakatar da yawace-yawacen ne daga karfe 7 na almuru sai zuwa karfe 5 na asuba a garuruwan biyu, dama kauyukan su baki daya. Sauran sassan Jihar Adamawa kuwa, dokar tana nan ne daga karfe 11 na dare zuwa 5 na Asuban kowace rana.

Daga farko dai rundunar ta sanar ta kafafen labaran cikin gida cewa matakin na jihar ne baki daya, amma daga bisani ta tabbatar Michika da Madagali ne ta sakewa dokar.

A wani labarin kuma a maƙociyar Jihar Adamawar, wato jihar Borno, ana fargabar mutane sama da 30 sun riga mu gidan gaskiya bayan wani hari da wasu 'yan bindiga da ake kyautata zaton 'yan Boko Haram ne suka kai a daren jiya a kauyen Mainok da ke kusa da Beni Sheikh.

Mazauna garin sun bayyana cewa ‘yan bindigan sun shiga garin ne sanye da kayan sarki irin na Soji inda suka budewuta kan mai uwa da wabi da manyan bindigogi.

Ya zuwa yanzu dai Hukumomi ko jami'an tsaro ba su ce komai ba kan wannan hari kuma babu wata kungiya da ta dauki alhakin kai harin.

Mawallafiya: Pinaɗo Abdu Waba
Edita: Muhammad Nasiru Awal