An soma yin jana'izar Muhammad Ali
June 9, 2016Talla
Sama da 'yan jaridu dubu biyu ne da masu ɗaukar hoto daga ƙasashen duniya za su halarci wannan jana'iza da za a yi yau Alhamis da gobe Jumma'a.Tare da halarta wasu daga cikin shugabanin ƙasashe a ciki har'da na Turkiyya Recep Tayib Erdogan.
Shugaba Barack Obama ba zai samu damar halarta jana'izarba saboda wani uzirin da ke gareshi sai dai zai tura wakili.Muhammad Ali ya rasu a ranar Jumma'a da ta gabata yana da shekaru 74,kuma tun daga shekara ta 1984 ya fara jinya cutar zanzzanar jiki watau Parkison