1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

An soma shari'ar harin Westgate a Kenya

January 15, 2014

Alƙalai sun fara sauraron wasu mutanen huɗu 'yan Somaliya waɗanda ake zargi da taimaka wa wasu 'yan ta'adda wajen kai hare-hare a kan wasu kantunan a Kenya a bara.

https://p.dw.com/p/1Ar1u
Kenia Vier Angeklagten Westgate Anhörung
Hoto: James Shimanyula

An soma fara sauraron ƙaran ne da wani sojin da ke gadi a kantunan na Westgate a lokacin da harin ya faru a ranar 21 ga watan Satumba na shekarar bara. Mutumin mai sunan Stephen Juma wanda ya shaida wa kotun cewar yana yin ban hannu na zirga-zirga motoci a gaban cibiyar kasuwanci a lokacin da wata motar ta tsaya a gaban ginin, mutane uku suka fita daga cikinta suka kuma shiga cikin kanti. Ya ce lokaci kaɗan sai ya fara jin harbe-harbe bindigogi kafin daga bisani ya ce ya yi kiran 'yan sanda ta hanyar waya domin sanar da su.

Tababa a kan mutuwar maharan a cikin hare-haren

A yanzu dai mutanen guda huɗu waɗanda ake zargi da taimaka wa 'yan ta'addar waɗanda suka haɗa da Adan Mohamed Abidkadir Adan, da Mohamed Ahmed Abdi, da Liban Abdullah Omar da kuma Hussein Hassan Mustafah, su dukkaninsu 'yan asilin ƙasar Somaliya sun musunta zargin taimaka wa maharan a gaban kotun. Wanda a cikin farmakin da aka kai sama da mutane guda 60 suka rasa rayukansu yayin da wasu 200 suka jikkata. Wanda wasu ƙwararru a kan al'amuran tsaro suka ce maharan suma sun mutu a lokacin da ake yin harbe-harben a cikin kantunan tsakanin maharan da jami'an tsaro. Ko da shi ke ma wasu masana a kan al'amuran tsaro na yin tababa a kan cewar maharan sun mutu a cikin gumurzun. George Musamali wani ƙwararre ne a kan harkokin tsaro a ƙasar ta Kenya.

Kenia-Spurensuche
Jami'an tsaro a bakin kantunan WestgateHoto: Reuters

Ya ce : ''Har yanzu babu wasu hujjojin da ke tabbatar mana da cewar waɗannan maharan sun mutu a cikin lamarin an dai samu gawarwaki na mutanen guda huɗu a cikin tarkaccen gine-gine da suka ruguza, kuma kotu ta yi bincike sai dai har yanzu mu ba mu samu tabbacin a kan gwaje-gwaje na jinin da aka yi ba ,na mutanen don haka ba zamu iya cewar ba waɗannan gawarwaki da aka samu na mutanen ne.'' A lokacin da ake kai hare-haren waɗanda aka kwashe kwanaki huɗu ana yi , an ɗau hotunan na wasu daga cikin 'yan ta'addar suna buga waya tarho mutanen kuwa sune Mohammed Abdinur Said, da Hassan Abdi Dhuhulow wani ɗan Somaliya mai shekaru 23 wanda ya taɓa zama a ƙasar Nowai.

Kenya ta ce babu gudu babu ja da baya a kan maganar yaƙi a ta'addanci

Ƙungiyar Al Shabaab dai ita ce ta ɗauki alhakin kai harin domin yin ramuwar gayya ga ƙasar ta Kenya, wacce ta tura sojojinta tun a shekarun 2011 domin yaƙar aiyyukan ta'addanci na ƙungiyar ta Al Shaabab kuma ƙungiyar ta gargaɗi hukumomin Kenya da su janye sojojinsu. To amma shugaban na Kenya Uhuru Kenyatta ya ce babu gudu babu ja da baya. ''Mun je Somaliya ne domin taimaka wa ƙasar ta sake dawo da doka da oda, kuma sojojinmu za su ci gaba da tsayawa a ƙasar har sai mun sauke wannan nauyi.''

Uhuru Kenyatta Ansprache Rede
Shugaban ƙasar Kenya Uhuru KenyattaHoto: John Muchucha/AFP/Getty Images

Ana sa ran wannan shari'a da aka soma a yau za a kwashe kwanaki ana yinta domin tantance gaskiyyar abin da ya faru a hare-haren na Westgate wanda sakamakon rugujewar gine-ginen saboda tashin bama-bamai majiyoyin ƙasashen ƙetare suka ce addadin mutanen da suka mutu ya kai 94.

Daga ƙasa za a iya sauraron wannan rahoto

Mawalllafi: Kiti /Hassane Abdourahamane
Edita : Umaru Aliyu