An soma binciken Shugaba Ramaphosa
June 12, 2019Wata mai shari'a mai zaman kanta ta kasar ta Afirka ta Kudu Busisiwe Mkhwebane wacce aka dora wa nauyin sa ido kan yadda gwamnatin zartarwa ke tafiyar da ayyukanta ita ce ta sanar da bude binciken kan batun wasu kudaden gudunmawar yakin neman zabe da wani kamfani ya zuba wa shugaban kasar a lokacin yakin neman zabensa.
A baya dai shugaba Ramaphosa ya kare kansa yana mai cewa tallafin kudin Euro dubu 30 da kamfanin Bosasa ya bayar, ya ba da shi ne ga dansa Andile mai bayar da shawara ga kamfanin.
Mai shari'ar na zargin taka wasu dokoki na da'ar aiki da aka shinfidawa mambobin gwamnati. Shugaba Ramaphosa wanda ke kan karagar mulkin kasar yau shekara daya da rabi ya sha alwashin kawar da matsalar cin hanci da ta dabaibaye kasar da ma ta kasance dalilin tsige Shugaba Jacob Zuma daga kan mukaminsa.