An soki matakin Baharain
June 21, 2016Hukumar Majalisar Dinkin Duniya mai kula da kare hakkin dan Adam ta ce matakin gwamnatin kasar Baharain na kwace takardun izinin zama dan kasa ga wani babban malamin 'yan Shia ya saba dokokin kasashen duniya.
Wata mai magana da yawun hukumar ta bayyana cewar gwamnatin Baharain ta gaza bin dokokin da suka dace, domin haka matakin kwace takardun izinin zama dan kasa ga Sheikh Isa Qassim abu ne da ba za a amince ba. Hukumar ta bukaci gwamnatin ta sake duba matakin ganin kimanin mutane 250 aka kwace musu takardun izinin zama 'yan kasa ta hanyoyin da suka saba ka'ida.
Ita dai masarautar Baharain Muslmai mabiya tafarkin Sunni suke jagoranci, amma galibin mutanen kasar sun kasance Musulmai mabiya tafarkin Shi'a. Kuma gwamnatin ta zargi malamin Sheikh Isa Qassim da neman tayar da zaune tsaye.