1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
SiyasaAfirka

An dage zaben Somaliya

February 6, 2021

An soke zaben ranar Litinin da aka tsara a Somaliya abin da ya bai wa Shugaba Mohammed Abdullahi Farmejo damar ci gaba da rike madafun ikon kasar har zuwa lokacin da ba a tantance ba.

https://p.dw.com/p/3ozd7
Dschibuti Einweihung Internationale Freihandelszone
Hoto: Getty Images/AFP/Y. Chiba

An dakatar da gudanar da zaben shugaban kasa da na 'yan majalissu da aka shirya gudanarwa ranar Litinin mai zuwa a Somaliya.

Soke zaben da aka yi a wannan Asabar zai bai wa Shugaba Mohamed Abdullahi Farmajo damar ci gaba da jan ragamar mulkin kasar duk kuwa da cewa sauran kwanaki 6 kachal wa'adin mulkinsa ya kawo karshe.

Dama dai Farmajon na cikin jerin 'yan takara da ke zawarcin kujerar shugaban kasar na wani wa'adin shekaru 4 nan gaba.

An shirya gudanar da babban zaben kasar ne a ranar Litinin mai zuwa 8 ga wata Febrairu. Sai dai Somaliya ta kwashe shekaru sama da 30 ba ta gudanar da zabe gama gari ba, inda wasu kwamintin amintattu mai mutane 51 ne ke zaben shugaban kasa.